仰望耶稣
1既然有这么多见证人像云彩一般围绕着我们,我们就要放下一切重担,摆脱容易缠累我们的罪,以坚忍的心奔跑我们前面的赛程, 2定睛仰望为我们的信心创始成终的耶稣。祂为了摆在前面的喜乐,就轻看羞辱,忍受了十字架的痛苦,如今已坐在上帝宝座的右边。 3你们要思想忍受罪人如此顶撞的主,免得疲倦灰心。
爱的管教
4其实你们与罪恶搏斗,还没有抵挡到流血的地步。 5你们难道忘了那像劝勉儿子一样劝勉你们的话吗?“孩子啊,不可轻视主的管教,被祂责备的时候也不要灰心。 6因为主管教祂所爱的人,责罚12:6 “责罚”希腊文是“鞭打”之意。祂收纳的儿子。”
7你们要忍受管教,上帝对待你们如同对待自己的儿子。哪有儿子不受父亲管教的呢? 8做子女的都会受管教,如果没人管教你们,那你们就是私生子,不是儿子。 9再者,我们的生身父亲管教我们,我们尚且敬重他们,何况是万灵之父上帝管教我们,我们岂不更要顺服祂并得到生命吗? 10我们的生身父亲是按自己以为好的标准暂时管教我们,但上帝是为了我们的益处而管教我们,使我们可以在祂的圣洁上有份。 11被管教的滋味绝不好受,当时都很痛苦,但事后那些受过管教的人会收获公义和平安的果子。 12所以,你们要举起下垂的手,挺直发酸的腿, 13修直脚下的路,使瘸腿的人不致扭伤脚,反得痊愈。
切勿违背上帝
14你们要尽力与大家和睦相处,并要追求圣洁的生活,因为不圣洁的人不能见主。 15你们要谨慎,以免有人失去上帝的恩典,长出苦毒的根扰乱你们,玷污众人。 16要小心,免得有人像以扫那样淫乱、不敬虔。他为了一时的口腹之欲,卖了自己长子的名分。 17你们知道,他后来想要承受父亲对长子的祝福,却遭到拒绝,虽然声泪俱下,终无法使父亲回心转意。
18你们并非来到那座摸得到、有火焰、乌云、黑暗、狂风、 19号角声和说话声的西奈山,听见这些声音的人都哀求不要再向他们说话了。 20因为他们承担不了所领受的命令:“即便是动物靠近这山,也要用石头打死它!” 21那情景实在可怕,就连摩西也说:“我吓得发抖。”
22但你们现在来到了锡安山,永活上帝的城邑,天上的耶路撒冷,欢聚着千万天使的地方。 23这里有名字记录在天上的众长子的教会,有审判众人的上帝和已达到纯全的义人的灵魂, 24还有新约的中保耶稣和祂所流的血。这血比亚伯的血发出更美的信息。
25你们必须谨慎,切勿拒绝对你们说话的上帝。因为以色列人违背了在地上警戒他们的人,尚且逃脱不了惩罚,何况我们违背从天上警戒我们的上帝呢? 26那时上帝的声音震动了大地,但现在祂应许说:“再一次,我不单要震动地,还要震动天。” 27“再一次”这句话是指上帝要挪去可以被震动的受造之物,使不能被震动的可以长存。 28那么,既然我们承受的是一个不能被震动的国度,就要感恩,用虔诚和敬畏的心事奉上帝,讨祂喜悦。 29因为我们的上帝是烈火。
1Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. 2Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. 3Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.
Allah yakan hori ’ya’yansa
4Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna. 5Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya,
“Ɗana kada ka rena horon Ubangiji,
kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,
6domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,
yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”12.5,6 K Mag 3.11,12
7Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. 9Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! 10Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. 11Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.
12Saboda haka, sai ku ƙarfafa raunanan hannuwanku da gwiwoyinku marasa ƙarfi! 13“Ku shirya hanyoyi marasa gargaɗa saboda ƙafafunku,”12.13 K Mag 4.26 don kada guragu su daɗa gurguntawa, sai dai su warke.
Gargaɗi game da ƙin Allah
14Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji. 15Ku lura fa kada wani yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai yă tsira har yă kawo rikici, yă kuma ƙazantar da mutane da yawa. 16Ku lura kada wani yă zama mai fasikanci, ko marar tsoron Allah kamar Isuwa, wanda saboda ƙwaryar abinci ɗaya tak ya sayar da gādonsa na ɗan fari. 17Daga baya, kamar yadda kuka sani, sa’ad da ya nemi yă gāji wannan albarka, aka ƙi shi. Bai sami zarafin tuba ba, ko da yake ya nemi albarkan nan da hawaye.
Dutsen tsoro da kuma dutsen farin ciki
18Ba ku zo ga Dutsen Sinai12.18 Dutsen Sinai. Wato, inda Allah ya ba wa annabi Musa dokoki domin Isra’ilawa wanda ana iya taɓawa ba, ko ga wuta mai ci sosai, ko ga duhu baƙi ƙirin, ko 19ko busar ƙaho, ko ga irin wata murya mai magana da kalmomin da masu jinta suka yi roƙo kada su ƙara ji, 20domin ba su iya jimrewa da abin da aka umarta cewa, “Ko da ma dabba ce ta taɓa dutsen, dole a jajjefe ta da duwatsu.”12.20 Fit 19.12,13 21Ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake, har Musa ya ce, “Ina rawar jiki don tsoro.”12.21 Dubi M Sh 9.19.
22Sai dai kun zo ne ga Dutsen Sihiyona, ga Urushalima ta sama, birnin Allah mai rai. Kun zo ga dubu dubban mala’ikun da suke cikin taron farin ciki, 23kun zo ga ikkilisiyar ɗan fari, waɗanda sunayensu suna a rubuce a sama. Kun zo ga Allah, alƙalin dukan mutane, kun kuma zo ga ruhohin mutane masu adalci da aka mai da su cikakku. 24Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila.
25Ku lura fa kada ku ƙi wanda yake magana. Gama in su ba su tsira sa’ad da suka ƙi wanda ya gargaɗe su a wannan duniya ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi daga Sama? 26A lokacin nan muryarsa ta jijjiga duniya, amma yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau sau ɗaya tak zan ƙara jijjiga ba duniya kaɗai ba, amma har ma da sammai.”12.26 Hag 2.6 27Wannan magana “sau ɗayan nan” sun nuna, kawar da abin da za a iya jijjigawa, wato, ƙirƙiro abubuwa, saboda abubuwan da ba a iya jijjigawa, su kasance.
28Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro, 29gama “Allahnmu wuta ne mai cinyewa.”12.29 M Sh 4.24