哥林多前书 14 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

哥林多前书 14:1-40

论讲道和说方言

1你们要追求爱,也要切慕属灵的恩赐,尤其是做先知讲道的恩赐。 2人说方言,是对上帝说的,并非对人说的,因为没有人听得懂,他是在心灵里述说各样的奥秘。 3但先知讲道是对人讲的,为了要造就、鼓励、安慰人。 4说方言只是造就自己,但做先知讲道是造就教会。 5我希望你们都能够说方言,不过,我更希望你们都能做先知讲道。说方言的不如做先知讲道的重要,除非把方言翻译出来,使教会得造就。

6弟兄姊妹,如果我到你们那里只说方言,不讲解有关上帝的启示、知识、预言、教导,我对你们有什么益处呢? 7就连没有生命的箫和琴,如果发出的声音杂乱无章,谁能知道所吹所弹的是什么曲子呢? 8如果号声不清楚,谁会预备打仗呢? 9同样,除非你们讲出清楚的信息,不然听见的人怎能明白呢?那岂不等于对空气说话吗? 10世上有各种语言,却没有一种是毫无意义的。 11如果有人对我说话,我却不明白他的语言,我们彼此就成了语言不通的人。 12你们也是一样,既然渴慕属灵的恩赐,就应该多多追求造就教会的恩赐。

13所以说方言的人应当祈求能把方言翻译出来。 14如果我用方言祷告,那是我的灵在祷告,但我的悟性没有发挥作用。 15那么,我该怎么做呢?我要用灵祷告,也要用悟性祷告;我要用灵歌唱,也要用悟性歌唱。 16否则,如果你在聚会中用方言14:16 本处“方言”希腊文是“灵”。来感恩,在座不懂方言的人不明白你在说些什么,怎能在你感恩的时候说“阿们”呢? 17你的感恩表达得固然美好,无奈不能造就别人。

18感谢上帝,我说方言比你们众人都多。 19但在教会中我宁可用悟性说五句教导人的话,胜过说万句别人不懂的方言。

20弟兄姊妹,你们的思想不要像小孩子,要长大成熟,但在罪恶的事上要像婴孩。 21律法书上记载:

“主说,‘我要借着讲陌生语言的人和外邦人的口向这些子民说话。

虽然如此,

他们仍然不听从我。’”

22由此可见,讲方言不是显给信徒的标记,而是显给非信徒的标记;但先知讲道是显给信徒的标记,不是显给非信徒的标记。 23所以,如果你们在聚会中,全体信徒都说方言,偶然有不懂方言的人或非信徒进来,他们岂不会说你们全都疯了吗? 24但如果你们都做先知讲道,偶然有非信徒或是不懂方言的人进来,他会醒悟到自己的罪,良心受到谴责, 25心中的秘密也会显露出来,便会俯伏敬拜上帝,说:“上帝真的在你们当中!”

聚会的原则

26那么,弟兄姊妹,你们该怎么做呢?你们聚会的时候,不管是唱诗、教导、讲启示、说方言或翻译方言,都应该是为了造就人。 27如果有人要说方言,应当只限于两个人,最多三个,要轮流说,而且要有人把它翻译出来。 28如果没有人翻译,说方言的人就当在聚会中闭口不言,只向自己和上帝说。

29做先知讲道的也应该限于两三个人,其他的人应当慎思明辨。 30但如果上帝的启示临到在座的其他人,正在讲的人要停下来, 31这样大家都可以轮流讲道,人人都可以得到教导和勉励。 32先知的灵受先知控制, 33因为上帝不是叫人混乱的上帝,而是赐人平安的上帝。

34正如圣徒的各教会一样,妇女14:34 妇女”也可译为“妻子”。在聚会中要保持安静,因为她们不可以发言,总要顺服,正如律法书所说的。 35如果她们想要学什么,可以在家问自己的丈夫,因为妇女在聚会中发言是可耻的。 36难道上帝的道是出自你们哥林多人吗?难道上帝的道单单传给了你们吗? 37如果你们当中有人自认为是先知或属灵的人,他就应该知道我现在所写的是主的命令。 38如果有人对此视而不见,不必理会他。

39所以,我的弟兄姊妹,你们要切慕做先知讲道,也不要禁止说方言。 40但无论做什么事,都要按规矩,有次序。

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 14:1-40

Baye-bayen annabci da kuma na harsuna

1Ku bi halin ƙauna kuna kuma marmarin neman baye-bayen ruhaniya, musamman baiwar annabci. 2Gama duk wanda yake magana da wani harshe14.2 Ko kuwa wani yare; haka ma a ayoyi 4, 13, 14, 19, 26 da 27 ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Tabbatacce, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne. 3Amma duk wanda yake annabci, yana magana ne da mutane domin yă gina su, yă ƙarfafa su, yă kuma yi musu ta’aziyya. 4Wanda yake magana da wani harshe kuwa, kansa yake gina, amma mai annabci, ikkilisiya ce yake gina. 5Zan so kowannenku yă yi magana da harsuna, sai dai zan fi so ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara don ikkilisiya ta ginu.

6To, ’yan’uwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba? 7Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa? 8Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi? 9Haka yake sa’ad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai. 10Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da ma’ana. 11To, in ban gane ma’anar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni. 12Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya.

13Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara. 14Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba. 15To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina. 16A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba? 17Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.

18Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka. 19Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe.

20’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya. 21A cikin Doka yana a rubuce cewa,

“Ta wurin mutane masu baƙin harsuna

da kuma ta leɓunan baƙi

zan yi magana da waɗannan mutane,

amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,”14.21 Ish 28.11,12

in ji Ubangiji.

22Harsuna fa alama ce ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa ga masu bi ne ba ga marasa bi ba. 23Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da waɗansu harsuna, sai waɗansu jahilai ko waɗansu marasa bi suka shigo, ashe, ba za su ce kuna hauka ba? 24Amma in wani marar bi, ko jahili ya shigo sa’ad da kowa yana annabci, sai maganar kowa ta ratsa shi, za su shawo kansa yă gane cewa shi mai zunubi ne saboda abin da kowa yake faɗi, 25asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yă yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!”

Tsarin sujada

26Me za mu ce ke nan ’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya. 27In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yă fassara. 28In babu mai fassara, sai mai magana yă yi shiru a cikin ikkilisiya, yă yi wa kansa magana da kuma Allah.

29Annabawa biyu ko uku za su iya yin magana, sauran kuma sai su auna a hankali abin da aka faɗa. 30In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune, sai mai magana na farko yă yi shiru. 31Dukanku kuna iya yin annabci bi da bi, domin kowa yă sami koyarwa da ƙarfafawa. 32Ruhohin annabawa kuwa suna ƙarƙashin sarrafawar annabawa. 33Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka.

34Ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi. 35In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace tă yi magana a cikin ikkilisiya.

36Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso? 37In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yă gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne. 38In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.

39Saboda haka ’yan’uwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana magana da harsuna. 40Sai dai a yi kome daidai da kuma cikin tsari.