启示录 21 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

启示录 21:1-27

新天新地

1接着我看见一个新天新地,因为以前的天地都消逝了,海洋也不复存在了。 2我又看见圣城新耶路撒冷从天上的上帝那里降下,预备好了,像妆饰整齐等候新郎的新娘。 3我听见从宝座中传来响亮的声音说:“看啊!上帝的居所设立在人间,祂要与人同住。他们要成为祂的子民,上帝要亲自与他们同在,做他们的上帝。 4上帝要擦干他们所有的眼泪,再没有死亡、忧伤、哭泣和痛苦,因为以前的事都已成过去。”

5坐在宝座上的那位对我说:“看啊!我已经将一切都更新了。你要将这一切记录下来,因为这些话真实可信。” 6祂又对我说:“一切都成了!我是阿拉法,我是俄梅加;我是开始,我是终结。我要将生命泉的水白白赐给口渴的人。 7得胜者必承受这一切福分,我要做他的上帝,他要做我的儿子。 8至于那些胆怯的、不信的、行为可憎的、杀人的、淫乱的、行邪术的、拜偶像的和所有说谎的,他们的结局是被丢进硫磺火湖里,这就是第二次的死。”

新耶路撒冷

9七位天使手里拿着盛满最后七灾的七个碗,其中有一位对我说:“你来,我要将新娘,就是羔羊的妻子指给你看。” 10我被圣灵感动,天使带着我到一座高大的山上,将从天上的上帝那里降下的圣城新耶路撒冷指给我看。 11城中充满上帝的荣光,璀璨如贵重的宝石,晶莹如碧玉。 12-13城墙高大,有十二个城门,东、北、南、西每面三个门,每个城门都有一位天使把守,门上写着以色列十二支派的名字。 14城墙共有十二块基石,基石上刻着羔羊的十二位使徒的名字。

15那和我说话的天使拿了一根金量秆要丈量圣城、城墙和城门。 16圣城是正方形的,长宽相等。天使用量秆丈量那城,长、宽、高都是两千二百公里21:16 两千二百公里”希腊文是“一万二千司他町”。17他又丈量了城墙,按人的尺寸来算是六十五米21:17 六十五米”希腊文是“一百四十四肘”。厚。 18城墙是用碧玉砌成的,城本身是用纯金造的,跟玻璃一样明净。 19城墙的基石用各种宝石装饰:第一块基石是碧玉,第二块是蓝宝石,第三块是绿玛瑙,第四块是绿宝石, 20第五块是红玛瑙,第六块是红宝石,第七块是橄榄石,第八块是水苍玉,第九块是黄宝石,第十块是翡翠,第十一块是紫玛瑙,第十二块是紫晶。

21十二个城门是用十二颗珍珠造的,每一个城门都是一颗珍珠,城中的街道是纯金的,好像透明的玻璃一样。

22我看见城中没有圣殿,因为全能的主上帝和羔羊就是圣城的殿。 23圣城里不需要太阳和月亮的光照耀,因为有上帝的荣光照耀,羔羊就是圣城的灯。 24万民要在圣城的光中行走,地上的君王也要将他们的荣耀带进圣城。 25城门整天都开着,那里没有黑夜。 26人们将列国的荣耀和尊贵带进圣城。 27所有污秽的、做可憎之事的、撒谎的都不得进入圣城。唯有名字记录在羔羊的生命册上的人才有资格进去。

Hausa Contemporary Bible

Ruʼuya ta Yohanna 21:1-27

Sabuwar sama da sabuwar duniya

1Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”

5Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”

6Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. 7Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. 8Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”

9Ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.” 10Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah. 11Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar lu’ulu’u mai daraja sosai, kamar yasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi. 12Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma mala’iku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila. 13Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma. 14An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon.

15Mala’ikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa. 16Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke. 17Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga ma’aunin mutum, wanda mala’ikan ya yi amfani da shi. 18An yi katangar da yasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. 19Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi yasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu, 20na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya yasin, na goma sha biyu kuma ametis. 21Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.

22Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin. 23Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin. 24Al’ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin. 25Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba. 26Za a kawo ɗaukaka da girmar al’ummai a cikin birnin. 27Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.