使徒行传 24 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

使徒行传 24:1-27

保罗在腓利斯面前受审

1五天后,大祭司亚拿尼亚带着几个长老和一位叫帖土罗的律师下到凯撒利亚,向总督控告保罗2保罗被传来后,帖土罗指控他说:“腓利斯大人深谋远虑,在大人的领导下,国中有许多改革,我们常享太平。 3我们对大人的恩德感激不尽。 4我不敢耽误大人太久,只求大人容我们简单叙述。 5我们发现这个人惹事生非,到处煽动犹太人闹事。他是拿撒勒教派的一个头目, 6企图玷污圣殿,被我们抓住了。我们想按照犹太律法处置他, 7不料吕西亚千夫长却硬把他从我们手中抢走, 8并命令告他的人到大人这里来。24:8 有古卷无“我们想按照犹太律法处置他,不料吕西亚千夫长却硬把他从我们手中抢走,并命令告他的人到大人这里来。”大人亲自审问他,就会知道我们告他的事了。” 9在场的犹太人也随声附和,表示这些事属实。

保罗的申辩

10总督点头示意保罗可以发言,于是保罗说:“我知道大人在犹太执法多年,我很乐意在你面前为自己辩护。 11大人明鉴,从我上耶路撒冷礼拜至今不过十二天。 12这些人根本没有见过我在圣殿、会堂或城里与人争辩,聚众闹事。 13他们对我的指控毫无根据。 14但有一点我必须承认,就是我依循他们称之为异端的道事奉我们祖先的上帝,我也相信律法书和先知书的一切记载, 15并且我与他们在上帝面前有同样的盼望,就是义人和不义的人都要复活。 16因此,我一直尽力在上帝和人面前都做到问心无愧。

17“我离开耶路撒冷已有多年,这次回来是带着捐款要周济同胞,并献上祭物。 18他们看见我的时候,我已行过洁净礼,正在圣殿里献祭,没有聚众,也没有作乱。 19当时只有几个从亚细亚来的犹太人在那里,如果他们有事要告我,应该到你这里告我; 20不然,请这些出庭的人指出他们在公会审问我时发现了什么罪。 21如果有,也无非是当时我站在他们当中喊了一句,‘我今天在你们面前受审与死人复活有关。’”

22腓利斯原本对这道颇有认识,于是下令休庭,说:“等吕西亚千夫长抵达后,我再断你们的案子。” 23他派百夫长看守保罗,给他一定的自由,也允许亲友来供应他的需要。

24几天后,腓利斯和他的妻子犹太土西拉一同来了,召见保罗,听他讲信基督耶稣的事。 25保罗讲到公义、节制和将来的审判时,腓利斯十分恐惧,说:“你先下去吧,改天有机会,我再叫你来。” 26腓利斯希望保罗贿赂他,所以经常召他来谈话。 27过了两年,波求·非斯都接任总督,腓利斯为了讨好犹太人,仍然把保罗留在监里。

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 24:1-27

Shari’a a gaban Felis

1Bayan kwana biyar sai Ananiyas babban firist ya tafi Kaisariya tare da waɗansu daga cikin dattawa da kuma wani lauya mai suna Tertullus, suka kawo ƙararsu game da Bulus a gaban gwamna. 2Sa’ad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa, “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa. 3Ko’ina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka. 4Amma don kada in ƙara gajiyar da kai, ina roƙonka ka yi haƙuri ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.

5“Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa 6har ma ya yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali; shi ya sa muka kama shi.24.6 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da shi, sun kuwa so su hukunta shi bisa ga doka. 7 Amma shugaban, Lisiyas, ya zo ya ɗauke shi daga hannunmu ƙarfi da yaji, 8 yana kuma umarci masu zarginsa su zo gabanka 8Ta wurin bincika shi da kanka za ka gane gaskiyar game da dukan waɗannan zargin da muke kawo a kansa.”

9Yahudawa ma suka goyi bayan zargin, suna tabbatar cewa waɗannan abubuwa haka suke.

10Da gwamna ya yi masa alama yă yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce, “Na san cewa ka yi shekaru da yawa kana mulki a wannan ƙasa; saboda haka ina farin ciki in kāre kaina. 11Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba. 12Masu zargina ba su same ni ina gardama da kowa a haikali, ko kuma ina tā da hankalin jama’a a majami’u ko kuwa wani wuri dabam a cikin birni ba. 13Ba kuwa za su iya tabbatar maka ƙarar da suke yi yanzu a kaina ba. 14Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa, 15ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka. 16Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.

17“Bayan ’yan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka. 18Ni tsarkake ne sa’ad da suka same ni cikin filin haikalin ina yin haka. Babu taro tare da ni, ba kuwa ina tā da hankali ba. 19Amma akwai waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya, waɗanda ya kamata suna a nan a gabanka su kawo ƙara in suna da wani a kaina. 20Ko kuwa waɗannan da suke a nan su faɗi laifin da suka same ni da shi sa’ad da na tsaya a gaban Majalisa, 21sai ko wannan abu ɗaya kaɗai da na ɗaga murya na faɗi yayinda nake tsaye a gabansu cewa, ‘A game da tashin matattu ake mini shari’a a gabanku yau.’ ”

22Sai Felis, wanda yake da cikakken sani game da Hanyar, ya ɗaga sauraron ƙarar. Ya ce, “In Lisiyas shugaban ƙungiyar soja ya iso, zan yanke muku shari’a.” 23Ya yi wa jarumin umarni yă tsare Bulus amma yă ba shi ’yanci yă kuma bar abokansa su lura da bukatunsa.

24Bayan ’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 25Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.” 26A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yă yi magana da shi.

27Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so yă biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku.