使徒行传 12 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

使徒行传 12:1-25

希律王的暴行

1那时,希律王下手残害教会的一些人, 2杀了约翰的哥哥雅各3他见这样做能取悦犹太人,便又在除酵节期间拘捕了彼得4把他关在监里,由四班卫兵,每班四人轮流看守,想等逾越节12:4 除酵节为期七天,逾越节是其中的第一天,参见出埃及记12章。过后当众惩办他。 5彼得被囚期间,教会都迫切地为他向上帝祷告。

彼得神奇出狱

6在被希律提审前一夜,彼得被两条铁链锁着睡在两个卫兵中间,门外警卫森严。 7忽然,有一位主的天使站在彼得身旁,监牢内一片光明,天使拍他的肋旁,把他叫醒,说:“赶快起来!”铁链就从他手上脱落下来。 8天使对他说:“束上腰带,穿好鞋子。”彼得一一照办。天使又说:“披上外衣,跟我来!” 9他跟着天使走出牢房,不知道这一切都是真的,还以为自己看到了异象。 10他们一路穿过第一道和第二道守卫,来到通往城里的铁门,那门竟自动打开了。他们就出来,走过一条街之后,天使便离开了彼得

11彼得这才如梦初醒,说:“现在我确定,主派了天使来救我脱离希律的魔掌,不让犹太人的期望得逞。” 12他清醒后,便到约翰·马可的母亲玛丽亚家,很多人正聚集在那里祷告。

13彼得在外面敲门,有一个叫罗大的婢女出来应门。 14她听出是彼得的声音,喜出望外,竟然没有开门就跑进去告诉大家:“彼得在门外!” 15他们说:“你一定疯了。”她坚持说:“是真的!”他们就说:“是他的天使吧!”

16彼得不住地敲门。他们开门看见他,都大吃一惊! 17彼得摆手示意他们安静,然后把主怎样领他出狱的经过告诉大家,又说:“把这事告诉雅各和其他弟兄姊妹。”交待完了,他便离开那里,往其他地方去了。

18天亮后,监狱的守卫发现彼得不见了,顿时一片骚动。 19希律派人四处搜捕,一无所获,于是亲自审问看守彼得的卫兵,下令处决他们。后来希律离开犹太,下到凯撒利亚,并住在那里。

希律的下场

20希律泰尔西顿的人非常恼火。于是,他们联合起来去见他,先取得宫廷总管伯拉斯都的支持,然后向他求和,因为他们两地需要从他的辖区获得粮食。

21到了约定的日子,希律穿上王袍,坐在宝座上向众人致词。 22致词完毕,众人齐声高呼:“这是神明在说话,不是凡人在说话!” 23希律没有把荣耀归给上帝,主的天使立刻惩罚他,他当场被虫子咬死了。

24上帝的道日见兴旺,越传越广。

25巴拿巴扫罗把款项送到以后,就带着约翰·马可耶路撒冷回去。

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 12:1-25

Kuɓuta mai banmamakin da Bitrus ya yi daga kurkuku

1Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu. 2Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi. 3Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti. 4Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa.

5Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa.

6A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa. 7Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.

8Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.” 9Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da mala’ikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani. 10Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Sa’ad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take mala’ikan ya bar shi.

11Sai Bitrus ya dawo hankalinsa ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki mala’ikansa yă cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”

12Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna addu’a. 13Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tă ji ko wane ne. 14Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!”

15Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, mala’ikansa ne.”

16Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki. 17Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma ’yan’uwa game da wannan,” sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri.

18Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus. 19Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su.

Mutuwar Hiridus

Sa’an nan Hiridus ya tashi daga Yahudiya ya tafi Kaisariya ya kuma yi ’yan kwanaki a can. 20Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu.

21A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi. 22Suka tā da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.” 23Nan take, domin Hiridus bai yi wa Allah yabo ba, wani mala’ikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu.

24Amma maganar Allah ta ci gaba da ƙaruwa ta kuma bazu.

An aiki Barnabas da Shawulu

25Sa’ad da Barnabas da Shawulu suka kammala aikinsu, sai suka komo daga12.25 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā zuwa Urushalima, tare da Yohanna, wanda ake kira Markus.