2 Коринфянам 7 – CARS & HCB

Священное Писание

2 Коринфянам 7:1-16

1Итак, возлюбленные, раз нам даны такие обещания, давайте же очистим себя от всего, что оскверняет наше тело и наш дух, завершая наше освящение в благоговении перед Всевышним.

Паул радуется вестям из Коринфа

2Откройте для нас ваши сердца! Мы ведь никого не обидели, никого не разорили, ни от кого не искали выгоды себе. 3Я говорю это не в осуждение, нет, – я ведь уже говорил вам, что вы в наших сердцах, и поэтому мы вместе и в жизни, и в смерти. 4Я очень верю в вас и горжусь вами! Вы ободряете меня настолько, что я радуюсь беспредельно, несмотря на все мои беды. 5Ведь даже когда мы пришли в Македонию, то не имели там покоя. Проблемы обрушились на нас со всех сторон: извне мы терпели нападки, а внутри нас одолевали страхи. 6Но Всевышний, утешающий тех, кто в унынии, утешил нас приходом Тита7:6 См. 2:12-13., 7и не столько самим его приходом, сколько рассказом о том, как вы приняли его. Он рассказал нам, как вы хотели бы меня увидеть, как вы сожалеете о происшедшем, рассказал о том, как рьяно вы вступились за меня, и это доставило мне огромную радость.

8Я не сожалею о том, что отправил вам послание, пусть оно и огорчило вас. Конечно, сперва я об этом пожалел, так как видел, что послание вас огорчило, пусть лишь на недолгое время, 9но сейчас я рад. Рад не потому, что вы чувствуете себя виновными, а потому, что ваша печаль привела вас к раскаянию. Ваша печаль была от Всевышнего, так что мы вам не причинили никакого вреда. 10Печаль от Всевышнего приводит к покаянию, которое, в свою очередь, ведёт ко спасению и уже не оставляет никакого места для сожаления. Но печаль этого мира ведёт лишь к смерти. 11Посудите сами: печаль от Всевышнего произвела в вас усердие, желание оправдаться, справедливое негодование на виновного, тревогу, жажду встречи, ревность, готовность наказать провинившегося. Вы полностью доказали свою невиновность в этом деле. 12Я писал вам не для того, чтобы обличить оскорбителя или же защитить оскорблённого7:12 Большинство толкователей думают, что под «оскорблённым» Паул имеет в виду самого себя.. Я хотел, чтобы вы сами видели, как искренне вы преданы нам перед Всевышним. 13И результат, который мы видим, радует нас.

Мы обрадовались не только той перемене, которая произошла в вас, но также радости Тита, что все вы успокоили его дух. 14Я прежде хвалил вас в разговоре с ним, и, к счастью, вы меня не подвели. Всё, что мы говорили вам, было верным, так же как оказалось верным и то, что мы, хваля вас, говорили Титу. 15Он всё больше и больше любит вас, когда вспоминает, как послушно вы внимали его словам и с каким благоговением и трепетом вы принимали его самого. 16И я рад, что во всём могу полагаться на вас!

Hausa Contemporary Bible

2 Korintiyawa 7:1-16

1Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.

Farin cikin Bulus

2Ku saki zuciya da mu. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba. 3Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa. 4Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.

5Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro. 6Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus, 7ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai.

8Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai. 9Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba. 10Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa. 11Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi. 12To, ko da yake na rubuta muku, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana. 13Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa.

Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka. 14Na yi taƙama da ku a wurinsa, ba ku kuwa ba ni kunya ba. Kamar dai yadda dukan abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka ma taƙamarmu a kanku a gaban Titus ya zama gaskiya. 15Ƙaunar da yake yi muku ya ƙaru ƙwarai, duk sa’ad da yake tunawa da biyayyarku duka, da kuma irin yawan bangirman da kuka nuna masa lokacin da kuka karɓe shi. 16Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.