1 Коринфянам 4 – CARS & HCB

Священное Писание

1 Коринфянам 4:1-21

Неразумность хвастовства посланниками Масиха

1Итак, принимайте нас как служителей Масиха, которым были вверены тайны Всевышнего. 2От тех, кому оказано такое доверие, требуется верность. 3Меня очень мало заботит, как вы или кто-то другой будет обо мне судить. Я и сам не сужу себя. 4Совесть моя чиста, хотя не это оправдывает меня. Но мой судья – Повелитель. 5Поэтому ни о чём не судите заранее, но ждите возвращения Повелителя. Он всё тайное сделает явным и обнажит скрытые намерения человеческих сердец, и тогда каждый получит от Него похвалу.

6Я говорю это, братья, обо мне и об Аполлосе ради вашего блага, чтобы вы на нашем примере постигли, что означает изречение: «Ничего сверх того, что написано»4:6 Скорее всего, здесь говорится о написанном в Священном Писании., и чтобы вы не хвастались кем-то одним, ставя его выше другого. 7Кто же делает тебя лучше других? Что у тебя есть своего, чего бы ты не получил от Всевышнего? Если ничего такого нет, то что же ты хвалишься подаренным?

8Вы, конечно же, думаете, что у вас уже всё есть, что вы уже богаты и уже без нас стали править вместе с Масихом! О, как бы я хотел, чтобы вы действительно уже правили, и тогда мы правили бы вместе с вами! 9Потому что мне кажется, что Всевышний выставил нас, посланников Масиха, как последних из людей, как осуждённых на смертную казнь, на всеобщее обозрение. Мы стали зрелищем для мира, для ангелов и для людей. 10Мы стали «глупцами» ради Масиха, вы же «мудрецы» среди Его последователей! Мы «слабы», а вы – «сильны»! Вас прославляют, а нас бесчестят! 11Мы по-прежнему испытываем голод и жажду, отсутствие одежды и терпим побои, у нас нет жилья, 12мы тяжким трудом сами зарабатываем себе на хлеб. Когда нас проклинают, мы в ответ благословляем; нас преследуют, а мы терпим. 13О нас говорят самое плохое, а мы отвечаем добром. До сегодняшнего дня мы как отбросы общества, всеми презираемые.

14Я пишу это не для того, чтобы устыдить вас, нет, я хочу вас предупредить как моих любимых детей. 15Хотя у вас тысячи учителей, которые следуют путём Масиха, у вас, всё же, не много отцов. Я же стал вашим отцом по вере в Ису Масиха через возвещение Радостной Вести. 16Поэтому умоляю вас: следуйте моему примеру. 17Для этого я и посылаю к вам Тиметея, моего дорогого и верного сына по нашей общей вере в Повелителя. Он напомнит вам о моём образе жизни как последователя Исы Масиха, которому я учу везде, в каждой общине верующих.

18Некоторые из вас возгордились, полагая, что я не приду к вам. 19Но я скоро приду к вам, если на то будет воля Повелителя4:19 Если на то будет воля Повелителя – это выражение широко распространено среди восточных народов, например: إن شاء الله («Иншалла», араб.), Qudai qalasa (каз.), Кудай кааласа (кырг.), Xudo xohlasa (узб.), Allah istәsә (азерб.), Hudaý halasa (турк.), Худо хоӽад (тадж.) и др., и тогда узнаю, чего стоят не слова этих гордецов, а их сила. 20Потому что Царство Всевышнего проявляется не в слове, а в силе. 21Выбирайте сами: прийти мне с розгой или же с любовью и в духе кротости?

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 4:1-21

Manzannin Kiristi

1Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah. 2Yanzu fa, ana bukatar waɗanda aka ba su riƙon amana, dole su zama masu aminci. 3Ƙaramin abu ne a gare ni a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a wata kotun mutane, ai, ko ni kaina ba na yanka wa kaina hukunci. 4Lamirina bai ba ni laifi ba, sai dai wannan bai mai da ni marar laifi ba. Ubangiji ne mai hukunta ni. 5Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.

6To, fa ’yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afollos saboda ku, don ku yi koyi da mu a kan abin da ake nufi da cewa, “Kada ku zarce abin da yake a rubuce.” Ta haka, ba za ku yi taƙama da wani mutum fiye da wani ba. 7Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi?

8Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna, kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku! 9Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin kallo ga dukan duniya, ga mala’iku da kuma mutane. 10Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu! 11Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida. 12Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre; 13in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

14Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku ’ya’yana ne, ƙaunatattu. 15Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara. 16Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni. 17Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.

18Waɗansunku suna tsammani ba zan zo wurinku ba har suna ɗagankai. 19Amma in Ubangiji ya yarda zan zo wurinku ba da daɗewa ba. Sa’an nan zan bincike ko masu wannan yawan ɗagan kan nan suna da wani iko. 20Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko. 21Wanne kuka fi so in na zo? Kuna so in tsananta muku ko in zama mai hankali da kuma sauƙinkai?